Hebrews 2

1Saboda haka, lalle ne mu kara mai da hankali musamman da abubuwan da mu ka ji, don kada mu yi sakaci, su sullube mana.

2Idan kuwa maganar nan da aka fada ta bakin mala’iku ta zama tabbatacciya, har kowanne keta umarni da rashin biyayya, suka gamu da sakamakonsu wanda ya kamace su, 3ta kaka za mu tsira, in mun ki kula da ceto mai girma haka? Domin Ubangiji da kansa, shi ne ya fara sanar da shi, wadanda suka saurare shi kuma suka tabbatar mana da shi. 4San’nan kuma Allah da kansa ya shaida ta wasu alamu, da abubuwan al’ajabai, da mu’ajizai iri iri, da kuma baiwar Ruhu Mai Tsarki dabam dabam da ya rarraba kamar yadda ya nufa.

5Ai ba ga mala’iku ba ne Allah ya sa mulkin duniyar nan da za a yi, wanda muke zance. 6Amma wani ya shaida a wani wuri cewa, ‘’Mutum ma menene, har da za ka tuna da shi? Ko dan mutum ma, har da za ka kula da shi.?

7Ka sa mutum ya gaza mala’iku; Ka nada shi da daukaka da girma. Bisa dukkan hallitta. 8Ka dora shi a kan dukkan halittarka, ka kuma mallakar da kome a karkashin sawayensa. Domin Allah ya mallakar da dukkan abubuwa a karkashinsa. Bai bar kome a kebe ba. Amma kuwa har a yanzu ba mu ga yana sarrafa dukkan abubuwa ba tukuna.

9Amma mun ga wani wanda dan lokaci aka sa shi ya gaza mala’iku, shine Yesu, an nada shi da daukaka da girma, saboda shan wuyarsa ta mutuwa, wanan kuwa duk ta wurin alherin Allah ne Yesu ya mutu saboda kowa. 10Saboda haka, ya dace ga Allah, shi da dukkan abubuwa suka kasance domin sa, ta gare shi, domin ya kawo ‘ya’ya masu yawa ga samun daukaka. Domin a kammala cetonsu ta wurin shan wuyarsa.

11Domin da shi mai tsarkakewar da kuma wadanda aka tsarkaken, duk tushensu daya ne. Saboda wanan dalili ne shi ya sa ba ya jin kunyar kiran su ‘ya’uwansa. 12Da yace, ‘’zan sanar da sunanka ga ya’uwana, a tsakiyar taronsu zan yabe ka da waka.‘’

13Har wa yau, yace, ‘’Zan dogara a gare shi.‘’ Da kuma ‘’Ga ni nan, ni da ‘ya’yan da Allah ya ba ni.‘’ 14Wato tun da yake ‘ya’yan Allah duk suna da nama da jini, Yesu ma ya dauki kamannin haka, ta wurin mutuwa ya hallakar da mai ikon mutuwa, wato Iblis. 15Ya kuma ‘yanta duk wadanda tun haihuwarsu suke zaman bauta sabo da tsoron mutuwa.

16Don hakika ba mala’iku yake taimako ba, a’a, zuriyar Ibrahim ne yake taimako. 17Saboda haka, lalle ne ya zama kamar yan’uwansa ta kowacce hanya, domin ya zama babban Firist, mai jinkai, mai aminci kuma na al’amarin Allah, ya kuma mika hadayar sulhu ta gafarta zunuban jama’a. Tun da yake Yesu ma da kansa ya sha wahala, sa’adda aka gwada shi, don haka, zai taimaki wadanda ake yi wa gwaji.

18

Copyright information for HauULB